Francois Hollande zai taron manema labaru

Image caption Zargin lalata ka iya kankane taron manema labarun

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande zai sanar da wasu tsare tsaren farfado da tattalin arzikin kasar a wani taron manema labarai da zai gabatar ranar Talata.

Sai dai ana hasashen cewa mai yiwuwa zargin da ake yi masa na lalata da wata fitacciyar jarumar fina-finai ya kankane taron manema labaran.

Ganawar dai ita ce ta farko da zai yi da 'yan jaridu tun bayan da wata jarida ta wallafa zargin.

Tuni dai aka kwantar da daduron shugaban kasar, Valerie Trierweiler a asibiti saboda matukar damuwar da ta yi bisa bayyanar rahotannin.

Karin bayani