Fargabar keta sirri a tsarin Gmail

Nan gaba kadan masu amfani da Gmail za su iya aika sakonni kai tsaye ga sauran masu amfani da shi, ko da kuwa ba su san adireshinsu na i-mel ba.

Sabon tsarin zai shafi duk wan da ke amfani da Gmail da kuma dandalin sada zumunta na Google+.

Sauyin ya kawo fargaba tsakanin masu rajin kare sirrin masu amfani da intanet, da su ka ce hakan zai iya bai wa mutane damar aike wa da sakonni ga wadanda ba su san su ba.

Google ya ce hakan zai saukaka wa masu amfani da shafin isar da sakonni ga abokanan huldarsu.

Sai dai mai rajin kare sirri Marc Rotenberg na kungiyar EPIC ya ce sabon tsarin tsarin na da matsalar gaske.

Saukin sadarwa

Masu amfani da Gmail za su ga jerin sunayen wadanda suke alaka da su a Google+ da zarar sun fara rubuta adireshi a shafinsu na tura sakonni, ko da kuwa ba su san i-mel din wanda suke son yi wa sakon ba.

Image caption Sakonnin masu amfani da Google+ za su isa adireshin Gmail kai tsaye.

A ranar Alhamis manajan Google David Nachum ya sanar da sabon tsarin da ya ce "zai sauwaka wa masu amfani da Gmail da Google+ saduwa da juna ta hanyar i-mel."

Masu amfani da shafin dai na da zabin kin karbar sabon tsarin tare da takaita wadanda za su iya aike musu da sako ba tare da amincewarsu ba.

Boyayyen adireshi

Mr Nachum ya ce za'a sanar da duk masu amfani da shafin game da sabon tsarin da kuma yadda za su tsame kan su daga cikinsa idan ba sa so.

Ya kuma ce ba za'a bayyana adireshin i-mel din ga masu amfani da Google+ ba har sai wanda aka tura wa sakon ya amsa.

Wannan sabon tsarin dai shi ne yunkuri na baya baya da Google ke yi na kara kusantar da tsarinta na i-mel da kuma dandalin sadarwar Google+.

Yanzu duk wanda ya yi rajistar Gmail za'a bude masa Google+ sai dai idan ya ki karba.