Iran za ta dakatar da shirin nukiliya

Image caption An cimma yarjejeniya tsakanin Iran da kasashen duniya

Jami'ai a Amurka da kuma Tarayyar Turai da Iran sun ce an cimma matsaya game da yadda za'a aiwatar da wata yarjejeniyar dakatar da shirin nukiliya da aka kulla a watan Nuwamba.

Kwararru daga kasashen duniya za su rinka dudduba kayayyakin nukiliyar kasar Iran akai-akai, wanda za'a soma daga ranar 20 ga Janairu.

Kuma an debar wa aikin wa'adin watanni shida, wanda daga nan ne kuma za a cimma wata cikakkiyar yarjejeniya ta karshe.

Ita kuwa Iran din, za'a sassauta ma ta wasu daga cikin takunkumin karya tattalin arzikin da aka sanya mata.

Karin bayani