"A cire kwamishinan 'yan sandan Rivers"

Image caption Gwamnan Rivers Rotimi Amaechi

Jam'iyyar adawa ta APC a Nigeria, ta bukaci a cire kwamishinan jihar Rivers da ke kudancin kasar bayan harbin Sanata Magnus Abe da ake zargin 'yan sanda sun yi a jihar.

Jam'iyyar ta ce 'yan sanda sun bude wuta a wani gangamin goyon bayan gwamnan jihar Rivers Rotimi Amaechi inda suka harbi sanatan da kuma shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar, Cif Tony Okocha.

Wata kungiya ta magoya bayan gwamnan jihar Ribas, Cif Rotimi Amaechi, mai suna 'Save Rivers Movement' ce ta shirya gangamin.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Ahmad Muhammad ya musanta wadannan zarge-zarge, inda ya ce; "Ba'a sanar da mu ba kuma ba'a nemi izinin 'yan sanda ba."

Sai dai mataimakin sakataren tsare-tsaren APC, Sanata Lawal Shuaibu ya ce babu wata doka a Nigeria da ta bukaci a nemi izinin 'yan sanda kafin shirya taron siyasa. Ya kuma yi zargin harbe-harben wata sharar fage ce kan yadda jam'iyyar PDP mai mulkin kasar za ta gudanar da yakin neman zaben 2015.