Manoman rani sun tafka asara a Kano

Image caption Dawowar ruwan ta zama tamkar ba da magani ga gawa

Manoman rani a kudancin Kano na cigaba da juyayin irin asarar da suka tafka sakamakon rufe ruwan da suke noman rani da shi, wanda yake tahowa daga madatsar ruwa ta Tiga.

Daruruwan manoma dai sun ce sun tafka asarar miliyoyin Naira sanadiyyar toshe ruwan, abin da haddasa bushewar amfanin gonakinsu.

Manoman dai sun yi zargin cewa hukumar Kogunan Hadeja da Jama'are ta rufe ruwan ba tare da sanar musu ba, abinda yasa ruwan da manoman ke ban-ruwan da shi ya kafe.

To sai dai hukumar ta Hadeja jama'are ta ce ta rufe ruwan ne domin yin gyara, kuma ta sanar da manoman gabanin fara aikin, wanda ta saba yi duk shekara

Karin bayani