Assad ya amince a shigar da kayan agaji

Image caption Shugaba Bashar al Assad na Syria

Ministan harkokin wajen Rasha, ya ce mai yiwuwa gwamnatin Syria ta bada damar a shiga da kayan agaji zuwa ga yankunan da aka yi wa kawanya.

Majalisar Dinkin Duniya ta sha nanata damuwarta a kan mawuyacin halin da mutanen suke ciki wadanda fada na wata da watanni tsakani gwamnati da dakarun 'yan tawaye ya rutsa da su.

Mr Lavrov ya furta haka ne bayan wasu shawarwari tare da takwaran aikinsa na Amurka John Kerry

Yace: "Gwamnatin Syria ta bayyana aniyarta ta bayar da sukuni ga ayarin motocin agaji zuwa garuruwan Yarmuk da Bassah".

Lavrov ya kara da cewar "Muna fatan su ma 'yan adawa su dauki irin mataki a kan wuraren da su ka yi wa kawanya".

Karin bayani