Red Cross ta ce jamaa na cikin bala'i a Syria

Wasu yara a Syria
Image caption Wasu yara a Syria

Shugaban kungiyar agajin Red Cross, Peter Maurer, ya bayyana mawuyacin halin da jama'a ke ciki a Syria a matsayin wani babban bala'i.

Bayan wata ziyara ta kwanaki ukku da ya kai a can, ya bayyana rikicin, wanda ya shafi miliyoyin mutane da cewar, ya kai intaha, kuma taimakon da ake yiwa mutane bai taka kara ya karya ba.

Wani mai magana da yawun kungiyar ta Red Cross a Damascus, Simon Schorno, ya ce akwai matukar muhimmanci a kyale kungiyoyin agaji su kai ga wadanda ke bukatar taimako.

Tun farko dai ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov ya ce gwamnatin Syria za ta iya kyale kungiyoiyin agaji su kai taimako ga al'ummomin da fada ya ritsa da su a cikin kasar.

Karin bayani