Gwamnoni ne jagororin APC - Masari

Image caption Mataimakin shugaban APC, Aminu Bello Masari

Mataimakin shugaban jam'iyyar adawa ta APC a Nigeria, Alhaji Aminu Bello Masari ya jaddada cewa gwamnoni ne jagororin jam'iyyar a jihohinsu.

Hakan ya biyo bayan rigingimun shugabanci da suka barke a jihohi da dama musamman tsakanin 'yan tsagin sabuwar PDP da kuma 'yan tsofaffin jam'iyyun ACN, ANPP da CPC.

Alhaji Aminu Masari ya ce inda babu gwamna kuma an kafa kwamitocin daidaitawa wadanda suka zabi shugabanninsu gwargwadon karfin tsofaffin jam'iyyun da suka yi hadaka.

Sai dai ya ce bayan rajistar 'yan jam'iyya a watan Janairu, za'a gudanar da zabubbukan shugabanci a watannin Fabrairu da Maris na bana.

Karin bayani