Kiristoci sun shirya Mauludi a Kaduna

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Musulmi a fadin duniya kan gudanar da Mauludi domin tuna haihuwar annabi Muhammadu Sallal lahu alaihi wa sallam

Wata kungiyar ci gaban al'umma ta Kirista a jihar Kaduna da ke arewacin Nigeria ta shirya bikin Maulidi domin tunawa da haihuwar annabi Muhammadu Sallal lahu alaihi wa sallama.

Kungiyar Peace and Reconciliation Foundation karkashin jagorancin Pastor Yohanna Baro ta ce manufarta ita ce samar da hadin kai tsakanin Musulmi da Kirista.

A lokacin bukukuwan Kirismeti dai kungiyar ta shirya wa malaman Musulunci liyafa domin bunkasa fahimtar juna tsakanin mabiya addinan biyu.

Jihar Kaduna dai na cikin yankunan Nigeria da ke fama da rikicin addini addini jefi-jefi.

Karin bayani