'Bam ya hallaka mutane 30 a Maiduguri'

Harin bam a Maiduguri Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Motoci goma ne da keke Napep biyar suka lalace a harin

Hukumomin Najeriya sun ce, mutane talatin ne suka hallaka, yayin da bam ya tarwatse a birnin Maiduguri na jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.

Lamarin ya faru ne a ranar Talata da rana a kasuwar Jagwal da ke cike makil da jama'a.

A cewar wasu rahotanni, an dana bam din ne a cikin wani keke Napep, yayin da kuma wasun ke cewa, an kushe shi ne a cikin wata jikka, aka yadda shi kusa da wata rumfa.

A wata hira da BBC, kakakin runduna ta bakwai ta dakarun sojin Nigeria a Maiduguri, Kanar Muhammed Dole, ya ce motoci kusan goma da keke-Napep biyar sun lalace, a sakamakon tashin bam din, kuma sun kama wani da ake zargi yana da hannu a tashin bam din.

Tuni dai kungiyar Jama'atu Ahli Sunna Lidda'awati wal Jihad da ake kira Boko Haram ta ce ita ta kai harin, wanda shine na baya-baya a hare-haren da ake kaiwa a arewacin Najeriyar, wadanda suka janyo mutuwar daruruwan mutane.

Karin bayani