Mutane 200 sun mutu a Sudan ta Kudu

Image caption Mutane na gujewa yakin Sudan ta Kudu a jiragen ruwa.

Fiye da mutane 200 da ke guje wa yaki a garin Malakal na Sudan ta Kudu sun nutse a kogin Nilu bayan da jirgin fiton da suke ciki ya kife, a cewar wani kakakin soji.

Malakal ne mashigar filayen hakar man fetur na lardin Upper Nile kuma ana shan gumurzu a garin cikin kwanakin nan.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutane 355,000 ne yaki tsakanin gwamnati da 'yan tawayen Sudan ta Kudu ya raba da matsugunnansu.

Ta kuma kiyasta cewa fiye da mutane 1,000 sun mutu a rikicin.