'Kawance tsakanin Assad da yammacin duniya'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kasashen yammacin duniya na tsaka mai wuya a Syria

Wani kakakin wata kungiyar 'yan adawa a Syria ya ce yaji mamakin rohotannin da ke cewa jami'an hukumomin leken asirin yammacin duniya na ziyartar Damascus don tattanawa a kan kulla kawance ta fuskar tsaro da gwamnatin Bashar Al- Assad.

Ya ce in dai maganar gaskiya ce, to kawancen zai jayo babbar matsala.

Mataimakin ministan harkokin wajen Syria ya shaida wa BBC cewa jami'an da suka ziyarci Syria sun je ne don tattaunawa a kan barazanar kungiyoyin kinshin Islama.

'Agaji'

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon ya ce rabin al'ummar Syria na bukatar agajin gaggawa.

Yana magana ne a Kuwait a wurin wani taron karo-karon kudi ga Syria inda su ke neman dala biliyan shida da rabi.

Kuwait ta yi alkawarin dala miliyan dari biyar kuma Amurka ta ce za ta taimaka da dala miliyan 380.

Ana taron ne a yayinda ake samun rohotannin dake cewa bala'in yunwa a wuraren da fadan yafi shafa.

Karin bayani