Ana ci gaba da kidaya kuri'u a Masar

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masar na hasashen samun nasara a zaben rabagardama

Ana ci gaba da kirga kuri'un da aka kada na zaben raba gardama kan sabon kundin tsarin mulki a Masar, inda gwamnatin kasar da ke samun goyan bayan Soji ke hasashen samun gagarumin nasara wanda zai tabbbatar da abinda suke so.

Ofishin Ministan harkokin cikin gida ya ce kuri'ar amincewa da daftarin zai kasance kashi 95%.

Shugaban kwamitin koli na zaben Nabil Sabih ya ce fitowar da mutane suka yi yafi wanda aka yi a zabukan baya inda mutane da yawa ba su fito ba.

Tun da fari jam'iyyar 'yan uwa musulmi ta kauracewa zaben a kokarin nuna adawa da hambarar da gwamnatin Muhammad Morsi.

Wakilin BBC a birnin Alkhahira ya ce sojoji su na bukatar mutane da yawa su fito dan kada kuri'a dan hakan zai bawa shugaban su Janar Abdel Fattah al-Sisi damar fitowa takarar shugaban kasa.

Karin bayani