Facebook ya kulla alaka da Yandex

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Facebook na fatan kara bunkasa yayin da ya ke fuskantar kasayya

Facebook ya amince ya bai wa Yandex - babban shafin matambayi baya bata na Rasha, damar amfani da bayanan da masu hulda da shi suka wallafa.

Yarjejeniyar ta ba Yandex damar amfani da bayanan masu hulda da Facebook a kasashen Rasha, Turkey, da kuma kasashen tsakiyar Turai da suka hada da Ukraine, Belarus da Kazakhstan.

Bayanan dai da Yandex zai yi amfani da su sun hada da batutuwan da 'yan kasashen ke wallafa wa a Facebook da martanin da abokan huldarsu ke mayar mu su. Sai dai ba za'a ba Yandex din damar bincika bayanan sirri ba.

Ana fatan shirin zai bai wa Yandex damar yalwata sakamakon bincikensa tare kuma da bunkasa adadin masu amfani da Facebook a Rasha.

"Nan ba da jimawa ba, sakamakon binciken Yandex zai bayyana abubuwan da mutane ke wallafa wa a Facebook da kuma martanin da ake mayar musu." A cewar wata sanarwa daga Yandex.

"Ana iya amfani da Yandex ke nan don gano abin da mutane ke cewa a Facebook game da manyan labarai, alal misali, ko kuma finafinai."

"Ingantaccen wakilci"

Facebook, wanda shi ne shafin sada zumunta ta intanet mafi girma a duniya, bai samu karbuwa ba a Rasha, inda shafukan cikin gida suka yi masa fintikau.

Kamfanin na kokarin samun shiga a kasashe masu tasowa domin rike matsayinsa a daidai lokacin da sauran shafukan sada zumunta ke barazanar kamo shi.

Yandex, wanda shi ne babban shafin matambayi baya bata na Rasha, ya ce zai ba abubuwan da suka yadu a Facebook muhimmanci wurin bayar da sakamakon bincikensa.

Ya ce bai wa kamfanin damar binciken bayanai cikin Facebook zai bai wa shafin "ingantaccen wakilci a sakamakon binciken Yandex."

"Muna jin cewa daya daga cikin muhimman ayyukanmu shi ne binciken shafukan sada zumunta ta yadda mutum zai iya lalubo abokansa ba tare da ya yi rajista a shafukan sada zumunta daya bayan daya ba."

Yandex dai bai bayyana farashin yarjejeniyar ta su da Facebook ba sai dai rahotanni da dama na cewa lamarin bai shafi kudi ba.

Karin bayani