An kashe mutane 38 a Iraq

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hare-haren bama-bamai na yawaita a Iraq

Mahukunta a Iraq sun ce bama-baman da suka fashe a babban birnin kasar da kuma harin kunar bakin wake a arewacin Bagadaza sun hallaka akalla mutane 38 tare da jikkata wasu da dama.

'Yan sanda sun ce wata mota da aka shake da bama-bamai ta fashe a kasuwar unguwar Shula dake arewacin Bagadaza sannan wata motar ta tarwatse a yankin Karrada dake tsakiyar birnin.

A garin Bhruz kuma da ke arewacin kasar, wani dan kunar bakin wake ya kai hari kan masu zaman makoki inda ya kashe akalla mutane 10 tare da jikkata wasu kusan 20.

Rikici na ci gaba da tsamari tsakanin 'yan Shi'a da Sunnah a Iraq shekaru biyu bayan da Amurka ta janye dakarunta daga kasar.