Isra'ila na neman sulhu da Amurka

Hakkin mallakar hoto
Image caption ISra'ila na kokarin rage rashin jituwarta da Amurka

Isra'ila na kokarin rage rashin jituwar da ta kunno kai tsakanin ta da babbar kawar ta Amurka.

Sabanin ya biyo bayan da ministan tsaron kasar Moshe Yaalon ya bayyana kokarin da Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ke yi na tabbatar da zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Palasdinu da cewa shirme ne kawai.

Sanarwar da ma'aikatar tsaron Isra'ila ta fitar da tsakar daren Laraba ta nemi afuwa akan duk wani batanci da furucin na Mr Moshe Yaalon ya yi wanda jaridun kasar suka wallafa.

Tun da fari ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta yi Allah wadai da wannan batu.

Karin bayani