An shiga rana ta biyu a zaben Masar

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An tsaurara tsaro wurin kada kuri'ar raba gardama.

Mutanen Masar na kada kuri'a a rana ta biyu kuma ta karshe ta zaben raba gardama kan sabon tsarin mulkin kasar.

An kashe mutane 11 yayin da 42 suka jikkata ranar Talata a rikici tsakanin 'yan sanda da magoya bayan shugaban kasa mai kishin Islama Muhammad Morsi, wanda sojoji suka hambarar da shi a watan Yulin da ya wuce.

Mahukunta sun yi gargadin cewa za su yi amfani da karfi wurin dakile duk wanda ya yi yunkurin kawo cikas ga zaben.

Gwamnatin da sojojin ke mara wa baya na fatan dimbin jama'a za su kada kuri'ar amincewa da sabon tsarin mulkin.

Karin bayani