PDP za ta yanke hukunci kan Bamanga

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Bamanga Tukur ka iya sauka daga mulki yau Alhamis

A Najeriya, a yau Alhamis ne ake sa ran majalisar zartarwar jam'iyyar PDP mai mulkin kasar za ta yanke hukunci a kan makomar shugaban jam'iyyar na kasa, Alhaji Bamanga Tukur.

Rahotanni dai sun ce shugaban jam'iyyar ya gabatar da wasikarsa ta yin murabus, kuma kwamitin zartarwar ne ke da ikon amincewa da ita.

Alhaji Bamanga Tukur na fuskantar matsin lamba daga 'ya'yan jam'iyyar cewa lallai sai ya yi murabus.

Gwamnonin Jam'iyyar dai na sahun gaba kan tursasa masa ya bar karagar mulkin bisa zarginsa da yin kama-karya wajen jagorancin jam'iyyar.

Karin bayani