Mazan Birtaniya na kallon lalata da yara

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Yada lalata da yara ta intanet ya zama ruwan dare a Brtaniya

Jami'an 'yan sanda a Birtaniya sun tarwatsa wani gungun mutanen da suke shirya cin zarafin yara ta hanyar lalata dasu a kasar Philippines tare da yada wa ta intanet.

An dai kama mutane 29 an kuma gano mutane sama da 700 da ake zargi.

Haka kuma an ceto yara 15 a kasar ta Philippines.

An fara bincike ne bayan da aka gano wani dan Birtaniya wanda ya sa iyalan wasu yara biyar a Philippines suka shiga lalatar ta yanar gizo.

Karin bayani