Bamanga Tukur ya rubuta takardar murabus

Shugaban jam'iyyar PDP a Nigeria Alhaji Bamanga Tukur ya rubuta takardar yin murabus daga mukaminsa.

Wata majiya mai karfi ta tabbatar wa BBC cewa Alhaji Bamanga Tukur ya rubuta takardar murabus din bayan matsin lamba da yake fuskanta daga wasu jiga-jigan jam'iyyar.

Rahotanni sun ce Alhaji Bamanga Tukur ya mikawa Shugaba Nigeria Dr Goodluck Jonathan takardar murabus din.

A yammacin yau ne ake sa ran kwamitin gudanarwa na Jam'iyyar PDP zai yi wani taro na musamman. Ana sa ran Shugaba Goodluck Jonathan zai shaidawa 'yan kwamitin matakin da Shugaban jam'iyyar ta PDP ya dauka.

Jam'iyyar PDP na fuskantar matsalolin cikin gida a karkashin mulkin Alhaji Bamanga Tukur abinda ya haddasa ballewar wasu gwamnoni biyar da 'yan majalisar wakilai da kuma wasu jiga-jigan jam'iyyar zuwa jam'iyyar adawa ta APC.

Karin bayani