Vatican na bada bayanin lalata da yara

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Papa Roma Francis a fadar Vatican

Wani kwamitin Majalisar Dinkin Duniya na sauraron bayanai a bainar jama'a daga wani babban jami'in fadar Vatican game da zargin fada-fada na cocin katolika na lalata da kananan yara.

Ana sa ran kwamitin majalisar kan hakkin yara zai tambayi dalilin da ya sa cocin ya kasa mika wadanda ake zargi ga 'yan sanda.

Ba'a dai taba titsiye jami'an Vatican game da wannan zargin a fili ba a baya, abinda ya sa masu fafutuka ke yaba wa da wannan binciken.

Sai dai fadar Vatican din ta ki amince wa ta bai wa majalisar sakamakon wani binciken cikin gida da ta gudanar game da malaman cocin dake fasikanci da kananan yaran.