"Amurka ta saci miliyoyin sakonnin salula"

Edward Snowden Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Edward Snowden

Tsohon jami'in leken asirin Amurkan nan Edward Snowden ya ce hukumar leken asirin kasar na tattara sakonnin wayar salula kusan miliyan 200 a kowacce rana a fadin duniya.

Wadanan bayanan na zuwa ne yayin da Shugaba Obama ke shirin sanar da sauye sauyen da aka yiwa aikace aikacen hukumar leken asirin Amurkar

Wani Editan BBC a arewacin Amurka yace shirye shiryen ayyukan hukumar leken asirin Amurkar da aka kwarmata ya janyo babban abin kunya ga gwamnatin Amurka

Sababbin bayanan wanda aka wallafa a Burtaniya sunce wani shirin hukumar leken asirin Amurkar da ake kira 'Dishfire' ya tattara bayanan mutane da suka hada da tafiye tafiyensu da kuma harkokin kudadensu