Nigeria za ta binciki zargin Obasanjo

Hakkin mallakar hoto
Image caption Obasanjo ya zargi Jonathan da horar da 'yan bindiga don kashe abokan hamayyar siyasa.

Hukumar kare hakkin bil'adama ta Nigeria ta nada kwamitin da zai binciki zargin da tsohon shugaban kasar, Mr Olusegun Obasanjo, ya yi cewa shugaba Goodluck Jonathan na horar da 'yan bindiga da zummar kashe abokan hammayarsa na siyasa.

Hukumar ta nada kwamitin ne bayan ministan shari'ar kasar ya bukace ta ta gudanar da bincike kan lamarin.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter, hukumar kare hakkin bil adama ta Nigeria, ta ce zargin da Mr Obasanjo ya yi na da matukar nauyi, don haka ne ta nada kwamitin mutane biyar domin biciken lamarin.

A watan jiya ne tsohon shugaba Nigeriar ya rubuta wa Mr Jonathan budaddiyar wasikar da ya zarge shi da aikata cin hanci da rashawa da kokarin ruguza kasar; zarge-zargen da Mr Jonathan ya musanta.

Karin bayani