Taliban:' Za mu sake mulkin Afghanistan'

Wani mayakin Taliban yana harba roka Hakkin mallakar hoto
Image caption 'Yan Taliban sun ce suna iko da yankuna da dama na Afghanistan

'Yan kungiyar Taliban da ke Afghanistan sun ce suna da kwarin gwiwa za su dawo kan karagar mulki nan ba da jimawa ba, kuma idan hakan ta tabbata, ba za su sassauta matsayinsu kan yadda suke tafiyar da mulki da kuma hukunta masu laifi ba.

Wani kakakin 'yan Taliban din, Zabiullah Mojahed, ya ce shariar musulunci tsari ne da ba ya canzawa ba, kuma wajibi ne a yi aiki da ita.

Sai dai kuma ya amince cewa dole ne a samu sauye sauye idan aka kwatanta da yadda ake a karkashin mulkin Taliban a Afghanistan kafun a kawadda su 2001.

Zabiullah Mojahed ya kara da cewa tuni kungiyarsu ke iko da yankuna da dama a kasar ta Afghanistan.

Karin bayani