An sanar da ranar zabe a Algeria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Abdelaziz Bouteflika

Shugaban Algeria Abdelaziz Bouteflika ya bada sanarwar cewa za a yi zaben shugaba kasar ranar 17 ga watan Afrilu wannan shekarar.

Shugaban mai shekaru 76 yana wa'adin mulkin sa ne a karo na ukku.

A ranar Alhamis ne Bouteflika ya dawo daga Asibiti a Faransa inda ake duba lafiyar sa bayan ya samu bugun jini a ara.

Jami'ayyar sa ta FLN ta amince ya sake tsaya mata takara a zaben dake tafe, amma kawo yanzu bai bayyana amincewar sa ba.

Karin bayani