Kotu ta ce a cigaba da tuhumar dan Abacha

Hakkin mallakar hoto nigeria at 50
Image caption Marigayi Shugaban Mulkin Sojin Nigeria, Janar Sani Abacha

Kotun kolin Nigeria ta umurci wata kotun tarayya dake Abuja ta ci gaba da tuhumar da take yi ma Mohammed Abacha watau babban dan Marigayi Shugaban Mulkin Sojin kasar a kan kudaden da ake zargin ya gada daga mahaifinsa alhali kuma kudi ne da ake zargin na sata ne.

A zaman da kotun karkashin jagorancin Mai shari'a Tanko Mohammed, alkalan Kotun sun yanke hukuncin cewa, iyalan Marigayi Shugaba Abachan ba su da wata kariyar tuhuma, kuma ko da shi kansa tsohon shugaban kasar ne, za a iya tuhumarsa muddin dai ya sauka daga kujerar shugabancin kasar.

Mohammed Abacha, babban dan marigayi shugaban Najeriyar ya shigar da karar ne a gaban kotun kolin yana neman ta dakatar da kotun tarayyar daga tuhumarsa a kan aikata miyagun laifukka na mallakar kudin da mahaifinsa ya bari suka gaada.

'Tuhuma'

Jerin laifukka dari da ashirin da ukku ne kotun tarayyar ta Abuja ke tuhumarsa da aikata wa wadanda suka shafi mallakar dukiyar da aka ce ta gwamnati ce wani ya saata.

Koda yake bai halarci zaman kotun ba, amma lauyansa ya yi tankiyar cewa na farko dai ba dukkan kudaden da Mohammed Abachan yake da su ba ne ya gaada daga mahaifinsa da har gwamnati ke kwace wa, kuma dokar soji ta 53 da gwamnatin Janar AbdusSalami Abubakar ta kafa, ta sa an kwace wani bangare na kudaden don haka bai kamata a tuhume shi ba.

Lauyan Abachan kuma ya yi tankiyar cewa mahaifin na sa tsohon shugaban kasa yana da kariya daga tuhuma don haka kamata ya yi hakan ta kasance ga iyalansa.

Karin bayani