India ta kaddamar da bindigar mata

India ta kaddamar da sabuwar bindiga ta mata, wacce aka rada wa sunan dalibar da wasu matasa suka yi mata fyade a Delhi a Disamban 2012 wacce hakan ya hallakata.

Jami'ai sun ce za ta taimakawa mata su kare kansu amma masu fafutuka na cewa hakan cin mutunci ne ga marigayiyar.

Janar Manajan kamfanin kera makamai na India, Abdul Hameed ya ce bindigar mai suna Nirbheek "karama ce, mara nauyi, kuma za ta iya shiga jakar hannu ta mata."

"Libarbar mai cin harsashi shida na iya harbin mutumin da ke nisan kafa 50 ba tare da kuskure ba."

Kodayake maza na iya sayen bindigar, ana tallata Nirbheek ne a matsayin "bindigar mata ta farko a India."

Kace-nace

An samo sunan Nirbheek ne daga Nirbhaya -wato lakabin da 'yan jaridun india suka bai wa dalibar da aka yi wa fyade a Delhi saboda dokar kasar ta hana ambatar sunan wacce aka yi wa fyade. Kalmomin biyu dai na nufin mara tsoro a harshen Hindi.

An dai fara kokarin yin bindigar tun kafin yi wa dalibar fyade a Delhi. Amma an gaggauta kammala aikin bayan da fyaden ya jawo zanga-zanga a fadin kasar.

A cikin motar haya ne 'yan daukar amarya suka yi wa dalibar, mai shekaru 23 fyade, tare da azabtar da ita sannan aka jefar da ita lokacin motar na tafe.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubunnan mutane ne suka yi makokin tunawa da Nirbhaya

Kaddamar da bindigar ya jawo kace-nace a India game da ko mallakar bindiga na iya kare mata daga fyade. Ram Krishna Chaturvedi, babbar jami'ar 'yan sandar gundumar Kanpur na ganin zai iya.

"Wannan dabara ce mai kyau. Idan kina da bindiga mai lasisi, za ta kara miki kwarin gwiwa tare da tsorata mahara," a cewarta.

Daga cikin matan dake fatan sayen Nirbheek har da Pratibha Gupta, wata matar aure kuma daliba a Kanpur.

Ta ce: "Ta yi tsada kwarai kuma samun lasisi na da matukar wuya," sai dai ta ce samun bindigar zai taimaka.

Kare kai

Bayan fyaden na Delhi dai, mata a biranen India sun shiga neman hanyoyin da za su kare kansu.

Gwamnatin India ta kaddamar da tsauraran dokoki game da fyade, tare da samar da karin 'yan sanda kan tituna, da kuma ware wata lambayar wayar neman agaji ta mata zalla.

Sai dai mata da yawa ba su amince da rundunar 'yan sandan da ta yi kaurin suna kan cin hanci da rashawa ba. Da yawansu sun shiga ajujuwan koyon fada da kare kai, tare da sayen barkonon feshi.

Amma duk da haka ana ci gaba da fyaden inda hukumar tattara bayanan laifuka ta India ta ce a kowane mintina 22 akan yi wa mace fyade a India.

Dangane da haka ne makeran Nirbheek suke ganin sun kawo kariya ga matan India.

Sai dai hankalin masu fafutukar yaki da yaduwar bindiga ya tashi game da wannan batu.

Tara kura

"Na yi mamaki kuma na fusata," in ji Binalakshmi Nepram, mai kungiyar tallafawa matan da aka harba da bindiga a jihar Manipur, wacce ta ce hakkin gwamnati ne ta tsare 'yan kasarta.

Nepram, wacce kungiyarta ta yi nazari kan amfani da bindiga a jihohin India takwas tsahon shekaru, ya ce mallakar bindiga "ba ya tsareki, sai dai ya kara miki hatsari."

Ta kara da cewa "A India, albashin mafi yawan mutane bai kai yawan kudin bindigar ba. Don haka babu yadda za'a yi su iya mallakarta."

Kiyasi dai ya nuna cewa akwai bindigogi miliyan 40 a hannun farar hula a India, wata duk duniya Amurka ce kawai tafi ta yawan bindigogi.

Mafi yawan wuraren taruwar jama'a a India ba su amince a shiga da bindiga ba - kuma ofisoshi, kantuna, sinima, da kasuwanni na da na'urorin gano karfe domin tabbatar da wannan doka.

Koda matar da aka yi wa fyade a Delhi ta mallaki bindiga, ba za ta yi amfani ba, saboda ta na koma wa gida ne bayan kallon fim a sinima a wani rukunin kantuna da ba za su kyale ta shiga da bindiga ba.

Kuma da ace tana da bindigar har ta yi nasarar harbe daya daga cikin maharan da sai ta tafi daurin rai da rai bisa laifin kisan kai.

Image caption Anita Dua ta mallaki bindiga amma ba damar amfani da ita

Anita Dua, mai fafutukar kare hakkin mata a Kanpur ta mallaki bindiga shekaru takwas da suka wuce amma ba ta taba samun damar amfani da ita ba.

Ta ce: " Na sayi bindigar ne domin kare kai, amma ba'a amincewa in shiga da ita wurare da dama, don haka yanzu tana kulle a gida na ta na tara kura."