'Mun shirya tattaunawa da 'yan tawaye'

Hakkin mallakar hoto telesur
Image caption Shugaba Bashar al-Assad na Syria

Gwamnatin Syria ta ce a shirye take ta kulla yarjejeniyar tsaigata wuta da dakarun 'yan tawaye, kuma ta bukaci Rasha ta shiga tsakani.

Ministan harkokin wajen Syria, Walid al-Mou'allem ya shaida wa manema labarai a Moscow cewar, ya bukaci takwaransa na Rasha, Sergie Lavrov ya shirya yadda za a dakatar da bude wuta a birnin Aleppo na Syriar.

Wannan ne karon farko da gwamnatin a Damascus ta dauki wannan matakin.

Mr al-Mo'allem ya ce gwamnatinsu a shirye take ta yi musayar fursunoni da wadanda ta ce 'yan bindiga sun sace su.

An soma yakin basasa ne a Syria a shekara ta 2011, kuma Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewar an kashe fiye da mutane 100,000 a tashin hankalin.

Karin bayani