'Museveni ya rangwata wa 'yan luwadi'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Yoweri Museveni

Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya ki ya amince da wani kudirin dokar dake tsananta hukunci ga masu luwadi.

Ya soki kakakin majalisar dokokin kasar saboda amincewa da kudirin dokar ba tare da samun amincewar kashi biyu cikin ukkun 'yan majalisar ba.

Shugaba Museveni ya bayyana masu luwadi da cewa mutane ne da dabi'ar su ta sabawa al'ada.

Ya kuma cewa za a iya raba su da dabi'ar idan aka tallafa masu.

Wakiliyar BBC ta ce shugaba Museveni na ganin cewa wasu 'yan kasar na yin luwadi saboda dan bunda ake basu..don haka ba za a iya hana dabi'ar ta fuskar doka ba.

Idan Shugaba Museveni yaki amincewa da kudirin dokar, to majalisa na da hurumin amincewa da shi idan ta samu amincewar kashi biyu cikin ukkun 'yan majalisa.

Karin bayani