Komla Dumor ya rasu

Marigayi Komla Dumor Hakkin mallakar hoto
Image caption Marigayi Komla Dumor

Mai gabatar da shirye-shirye na BBC, Komla Dumor ya rasu a gidansa dake nan London sakamakon ciwon zuciya.

Dan shekaru araba'in da daya, Komla ya soma aiki da sashen Afurka na BBC ne a shekara ta 2007, bayan ya shafe shekaru fiye da goma yana aiki a wani gidan rediyo a kasarsu Ghana.

Komla dai shi ne yake gabatar da shirin farko na talabijin da BBC take gabatarwa.

Peter Horrocks, daraktan sashen yada shirye-shiryen BBC zuwa kasashen waje, ya bayyana Komla Dumor a matsayin wani fitaccen dan jarida dake bada labaran da suka shafi kasashen Afurka.