Za a yi jana'izar Patrick Karegeya

Marigayi Kanal Patrick Karegeya
Image caption Marigayi Kanal Patrick Karegeya

Za ayi jana'izar tsohon babban jami'in hukumar leken asiri ta Rwanda, Kanal Patrick Karegeya a birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu

An samu gawar jami'in dan tawayen ne a wani Otel dake birnin Johannesburg a ranar daya ga watan Janairu.

A cewar 'yan sandan Afrika ta Kudu, akwai alamu na yakushi a wuyansa, abinda ya nuna cewar mai yiwuwa an shake shine har ya mutu.

Patrick Karegeyan dai yayi gudun hijira ne tun shekaru da dama da suka wuce.

Iyalansa da suka isa kasar Afrika ta kudun saboda jana'izar sa, na zargin gwamnatin Rwandan da hannu a mutuwar sa.

Baya ga iyalansa cikin masu halartar jana'izar har da 'yan jam'iyar adawar Rwanda National Congress wacce ya kafa a shekara ta 2010.

Har yanzu ba a samu labarin ainin abinda ya faru da shi a ranar jajibirin sabuwar shekarar.