Sojan gwamnatin Sudan ta Kudu sun kwaci Bor

'Yan kasar Sudan ta Kudu Hakkin mallakar hoto
Image caption Sojan Sudan ta Kudu sun kwaci garin Bor

Rundunar sojan Sudan ta kudu tace, dakarunta sun kwace iko da garin Bor mai muhimmanci.

Kakakin sojan kasar, Philip Aguer yace, dakarun gwamnati sun yi nasara a kan fiye da dakarun 'yan tawaye dubu goma sha biyar dake biyayya ga tsohon mataimakin shugaban kasar watau Riek Mashar.

Sai dai kuma garin na Bor, wanda shi ne babban birnin jihar Jonglei ya sha sauya hannu tsakanin 'yan tawaye da gwamnati tun daga lokacin da fada ya barke a Sudan ta kudu kusan wata guda da ya gabata.

Karin bayani