Kungiyar adawar Syria za ta halarci taron Geneva

'Yan tawayen kasar Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan tawayen kasar Syria

Babbar kungiyar adawa ta Syria ta kada kuri'ar amincewa ta halarci taron samar da zaman lafiya da za a yi a birnin Geneva cikin makon gobe.

Yayin taron da 'yan adawar suka gudanar a Turkiyya, gamayyar kungiyar hadaka ta kasar Syria ta kada kashi hamsin da takwas na yawan kuri'un da aka kada don amincewa da a halarci taron , duk kuwa da cewa karin wasu wakilai kusan hamsin sun kaurace.

Batun halartar taron zaman lafiyar a Geneva dai ya kawo rarrabuwar kawuna tsakanin 'yan adawar na kungiyar Syrian National Coliation.

Wasu dai na dagewa cewa, lallai sai an fitar da shugaba Bashar Al Assad daga lissafin kowacce gwamnatin rikon kwarya da za a kafa.

Wani babban jami'i a Majalisar gudanarwar kasar Syria Monzer Akbik ya shaidawa BBC cewa sun amincewa dakarun Free Syrian Army su aike da wakilan su wajen taron na Geneva.

Ya ce jiga-jigan dakarun Free Syrian Army sun aike da wasika wurin mutanen dake zaman tattaunawar, kuma an karanta wasikar.

Hakan na nufin kungiiyar gamayyar 'yan adawar su tabbatar cewa wakilan da zasu taron Geneva su hada da na Free Syrian Army, 'yan siyasa, kwararru da jami'an huddar diplomasiyya.