Tashin hankali na ci gaba a Tsakiyar Afrika

'Yan daba a jamhuriyar Tsakiyar Afrika Hakkin mallakar hoto
Image caption 'Yan daba a jamhuriyar Tsakiyar Afrika

Kwana guda kafin zaben majalisar wucin gadin jamhuriyar Afurka ta tsakiya ta zabi sabon shugaban kasar na rikon kwarya, tashin hankali yana karuwa a kasar.

Ana dai bada rahotannin zubar da jini a mafi yawan sassan kasar, kuma rundunar kiyaye zaman lafiya ta kasashen Afurka dake aiki a kasar tayi kashedin cewa, zaben na gobe zai iya haifar da karin tashin hankali a kasar.

Jiya Asabar dai Jamus ta ce, kasashen Turai ba zasu sa ido su bar Faransa ita kadai da kokarin kawo zaman lafiya a kasar ba.

Ranar Litinin ne dai kungiyar tarayyar Turai zata tattauna yiwuwar aika dakaru zuwa kasar.