Yunkurin sasanta 'yan tawaye a Syria

Tashin hankali a Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tashin hankali a Syria

Jagoran wata kungiya da ake dagantawa da Al Qaeda a Syria yayi kiran a sasanta tsakanin kungiyarsu da wasu kungiyoyin 'yan tawayen dake fada da su tsawon makonni.

Wani sako da aka ce, daga shugaban kungiyar yunkurin kafa daular musulunci a Iraqi da wasu kasashe dake makwataka da ita, Abubakar Al Baghdadi yayi kiran mabiya mazhabar Sunni dake yaki a Syria, su maida hankalinsu wuri guda domin yakar wadanda suka kira makiyansu, wato 'yan Shi'a.

Fada tsakanin kungiyoyin 'yan tawaye mabiya mazhabar Sunni yayi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da dubu cikin makonni biyun da suka gabata.