Maza biyar sun yi wa yarinya fyade

Image caption Zanen fuskar jagoran wadanda ake zargi da fyaden.

'Yan sanda a yankin Essex dake Ingila sun fara bincike kan fyaden da wata matashiya ta ce maza biyar sun yi mata shekaru uku da suka wuce.

Yarinyar mai shekaru 13 a lokacin, ta ce wani gungun maza masu shekaru 25 zuwa 35 ne suka yi mata fyaden a cikin wani lungu a garin Rayleigh ranar 24 ga Fabrairu, 2011.

Ta ce sun ja ta ne zuwa wani fili dake kusa da lungun, inda suka aikata masha'a da ita.

'Yan sandan sun ce ta kasa kai kara a lokacin ne saboda matukar tsorota da ta yi har sai bayan da ta sanar da mahaifiyarta a farkon watan nan.

Kwararrun jami'ai daga sashen bincike kan laifuffukan da suka shafi jima'i na rundunar 'yan sandan Essex sun tattauna da yarinyar, inda suka fitar da zanen fuskar babban wanda ake zargi da aikata laifin.

Neman bayani

Jami'in bincike Danny Cooper ya ce: "Wannan mummunar barna ce da mazaje biyar suka yi wa yarinyar da a lokacin shekarunta 13.

"Abin ya yi matukar razanata, kuma ta zauna cikin fargaba har sai lokacin da ta samu kwarin gwiwar sanar da mahaifiyarta abinda ya faru.

"Mu na neman taimako daga duk wanda yake da bayani game da faruwar lamarin ko kuma zai iya gane mutumin da ake nema daga fuskar da aka zana."

An dai baiyana jagoran wadanda ake zargin da cewa fari ne, mai tsawon kafa biyar da inci takwas, wanda yake da yawan gashin gira mai duhu.

Karin bayani