Yarjejeniya kan nukiliyar Iran

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tashar samar da makamashi ta Iran

Hukumar da ke kula da makamashin nukiliya ta majalisar dinkin duniya ta ce Iran ta fara takaita shirinta na samar da makamashin uranium a wani bangare na sharudan yarjejeniyar da aka kulla da ita domin cire mata takunkumin da aka kakaba mata.

Hukumar ta ce Iran din ta takaita hakan ne da fiye da kashi biyar cikin dari a wani yunkuri da ke nuna cewa za a iya samar da makamin nukiliya.

Yanzu haka dai masu binciken makamai na majalisar dinkin duniya za su samu karin damar shiga wuraren da ake sarrafa makaman.

Iran dai ta hakikance cewa, shirinta na makamashin nukiliya na zaman lafiya ne.

Shugaban hukumar da ke kula da makamashi ta Iran, Ali Akbar Salehi ya tabbatar da cewa sun dakatar da aikin da suke yi na samar da makamashin uranium.

Karin bayani