An nada Adamu Mu'azu shugaban PDP

Hakkin mallakar hoto muazu facebook
Image caption Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Alhaji Ahmed Adamu Muazu

Jam'iyyar PDP mai mulkin Nigeria ta nada tsohon gwamnan jihar Bauchi, Alhaji Ahmed Adamu Mua'zu a matsayin sabon shugabanta.

Adamu Mu'azu ya maye gurbin Alhaji Bamanga Tukur wanda ya yi murabus a makon da ya gabata, sakamakon matsin lamba a kan yadda yake jagorantar 'ya'yan jam'iyyar.

A taron koli na 'yan kwamitin zartarwar jam'iyyar PDP a Abuja, Gwamnan jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda ne ya gabatar da kudurin nada Adamu Mu'azu a yayin da Sanata Victor Ndoma Egba ya mara masa baya.

Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ne ya shugabanci taron jam'iyyar a daidai lokacin da PDP ke fuskantar rikicin cikin gida, abinda ya sa gwamnoni biyar koma wa jam'iyyar adawa ta APC.

Mu'azu zai shugabancin jam'iyyar har zuwa lokacin da jam'iyyar za ta gudanar da babban taron zaben sabon shugabanta.

Karin bayani