An fara shari'ar Ribery da Benzema

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Zahia Dehar ta yiwa 'yan wasan karyar ta balaga.

An gurfanar da fitattun 'yan kwallon Faransa biyu gaban kotu bisa zargin yin jima'i da karuwar da ba ta cika shekaru 18 ba.

Karuwar, wacce yanzu take da shekaru 21 ta ce Franck Ribery, dan kungiyar Bayern Munich ya sa an kai masa ita Jamus a 2009, a matsayin kyautar zagayowar ranar haihuwarsa.

Ta kuma ce an biya ta ta sadu da Karin Benzema da ke buga wasa a Real Madrid ta Spain.

Sai dai ta ce a lokacin ta yi musu karyar cewa ta balaga.

Benzema dai ya musanta zargin.

Shi kuwa Ribery ya tabbatar da saduwa da ita amma ya musanta cewa sai da ya biya.

Idan aka tabbatar da laifin, 'yan wasan biyu za su iya fuskantar daurin shekaru uku a gidan yari.