'Yan adawar Syria ba zasu je Switzerland ba

Hakkin mallakar hoto non
Image caption Gayyatar Iran ta janyo matsala

Babbar kungiyar 'yan adawar Syria ta dakatar da shiga cikin tattaunawar zaman lafiya da aka shirya yi a wannan makon a kasar Switzerland.

Ta dauki matakinne bayan da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-Moon ya gayyaci Iran don ta halarci tattaunawar.

Mr Ban ya ce Iran nada rawar da za ta taka wajen kawo karshen rikicin.

Amurka da Birtaniya da Faransa sun ce Iran ta fito fili ta goyi bayan kafa gwamnatin rikon kwarya a Syria, idan har tanason ta halarci bude taron a Geneva.

Iran ta amsa gayyatar majalisar dinkin duniya don ta halarci taron, amma ta yi watsi da batun gindaya wasu sharuda.

Daya daga cikin kungiyoyin 'yan adawar wato Syria National Coalition, ta ce Shugaba Bashar Al-Assad bai kamata ya taka wata rawa ba a makomar kasar a nan gaba.

Karin bayani