Tattaunawa ka'in da na'in a kan Syria.

'Yan adawar Syria
Image caption 'Yan adawar Syria

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki- Moon, ya ce ana cigaba da tattaunawa mai zurfi, bayan da babbar kungiyar adawa ta Syria ta janye daga halartar tattaunawar sulhun da za ayi a makon nan a Switzerland a kan Syriar.

Babbar jam'iyyar adawar ta Syria ta mayar da martani ne ga gayyatar da Mr Ban ya yi wa Iran, kan ta halarci kwarya-kwaryan taron tattaunawar zaman lafiyar wanda aka yiwa lakabi da Geneva Two.

Mai magana da yawun kungiyar ya shaidawa BBC cewa, bai kamata Iran ta halarci taron ba tun da ta na da sojoji a Syria wadanda ke goyon bayan Shugaba Assad.