Ana ci gaba da gwabzawa a Ukraine

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu zanga-zanga a Kiev

Ana cigaba da gwabzawa a Ukraine tsakanin masu zanga-zanga da ke kin jinin gwamnati da kuma 'yan sanda bayan wani mummunan rikici da aka yi cikin dare tun bayan rikicin siyasar da aka shafe makonni tara ana yi a kasar.

Masu zanga-zanga sun yi shinge da konannun motoci tare da jefa duwatsu da kuma bam din da suka yi da kan su yayin da jami'an 'yan sanda kuma suka bude wuta da harsashe na roba.

Shugaban kasar Viktor Yanukovych ya yi alkawarin kafa wata hukuma ta musamman domin nemo bakin zaren rikicin.

Ministocin harkokin wajen kasashen tarayyar Turai daga Sweden da Birtaniya sun zargi gwamnatin kasar da amincewa da dokokin da suka kira wadanda za su gallazawa ma su zanga-zanga.

Karin bayani