An sace fiye da mutane 50 a Afghanistan

Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Mayakan Afghanistan ba sa kai wa masu aikin kwance bama-bamai hari a baya.

Jami'an Afghanistan sun ce wasu da ba'a san su ba, sun sace fiye da farar hula 50 dake aikin kwance-kwance binnannun bama-bamai a yankin Herat dake yammacin kasar.

Wadanda aka sace maza ne 'yar kasar Afghanistan dake aiki karkashin kungiyar agajin Halo Trust ta Britaniya.

Jami'ai sun ce an sace mutanen ne a gundumar Pashtun Zargun.

Wasu mutane shida kuma sun tsere wa masu kamen bayan da suka yi musayar wuta.

'Yan bindigar Afghanistan dai ba sa kai farmaki kan fararen hular dake aikin kwance bama-bamai a gonaki da sauran yankunan al'umma.