An kashe wanda ya tsare mata a China

Image caption Mutumin ya ajiye matan ne a kurkukun karkashin kasa

Mahukuntan China sun kashe wani mutum da ya tsare mata shida a wani kurkukun karkashin kasa, sannan ya rinka lalata da su.

Li Hao ya kuma tilasta wa uku daga cikin matan su kashe wasu guda biyu.

Ma'aikacin gwamnatin ya yaudari matan ne suka bi shi gida sannan ya kulle su tsawon watanni biyu zuwa 21.

Mutumin ya sha yi wa matan fyade, ya kuma tilasta musu karuwanci, sannan kuma ya sa suka yin abubuwan batsa a gaban kyamarar daukar hoton bidiyo ta intanet.

An gano kurkukun da Li ya haka da kansa a birnin Luoyang ne bayan da daya daga cikin matan ta tsira.