Lagos ta hana busa taba a mahadar jama'a

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Sigari na barazana ga lafiyar al'umma amma kamfanoninta sun ce tana samar da aikin yi da bunkasa arziki.

Majalisar dokokin jihar Lagos ta zartar da dokar hana busa sigari a bainar jama'a.

Dokar ta haramta shan sigarin ne a wuraren da suka hada da dakunan karatu, gidajen adana kayan tarihi, gidajen wanka da bahaya, makarantu, asibitoci, motocin haya, da wuraren sayar da abinci, da sauran makamantansu.

Idan dokar ta fara aiki, za'a ci tarar wanda ya karyata N10,000 zuwa N50,000 ko kuma dauri a gidan yari.

Masana kiwon lafiya sun tabbatar sigari na barazana ga lafiyar al'umma sai dai kamfanonin da ke yinta na cewa ta na samar da aikin yi da bunkasa tattalin arzikin kasa.

Karin bayani