An damke 'yan ci-rani 1,500 a Malaysia

Image caption Wani dan ci-rani daga Burma a Malaysia

Gwamnatin kasar Malaysia ta damke 'yan ci rani fiye da 1,500 a yinkurinta na kawo karshen ayyukan bakin haure a kasar.

Hukumomin sun aike da dubban 'yan sanda don tsare 'yan kasashen waje dake aiki a cikin kasar ba tare da izini ba.

'Yan ci-rani daga kasashen Indonesia da Nepal wadanda ba suda takardun hukuma za a tasa keyarsu cikin kwanaki bakwai.

Akwai dubban 'yan ci-rani a kasar Malaysia wadanda aka yi wa rijista a cikin shirin bada afuwa na gwamnatin kasar.

Karin bayani