Za'a fara sabuwar shari'ar Morsi a Egypt

Image caption Muhammad Morsi na fuskantar sharia bayan hambarar da gwamnatinsa da sojoji suka yi.

Wata kotu a Egypt ta sa ranar 16 ga Fabrairu domin fara sauraron wata karar da ta shafi tsohon shugaban kasar Muhammad Morsi.

Wannan ce sharia ta uku da za'a yi wa tsohon shugaban kasar da sojoji suka hambarar a watan Yulin bara, bayan da zanga-zanga ta barke game da mulkin da yayi shekara guda ya na yi.

A wannan shari'ar, Mr Morsi da manyan jami'an kungiyar 'yan uwa Musulmi na fuskantar tuhumar keta tsaron kasa na ta hanyar hada baki da Iran da kuma 'yan bindiga masu kishin Islama da suka hada da Hamas da Hezbollah.

Haka kuma ana zarginsu da shirya hare-haren ta'addanci a kasar bayan kifar da gwamnatin Mr Morsi.