Jonathan zai nada sababbin ministoci

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Goodluck na neman amincewar majalisar dattawa domin nada sababbin ministoci 12

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya aike da sunayen mutane 12 ga majalisar dattawan kasar domin neman amincewar nada su ministoci.

Mutanen sun hada da tsohon mai bada shawara kan harkokin tsaro na kasar, Janar Aliyu Gusau mai ritaya, daga jihar Zamfara, tsohon jakadan Nigeria a Ghana, Sanata Musiliu Obanikoro daga jihar Lagos, da tsohon gwamnan jihar Adamawa, Boni Haruna.

Sauran sun hada da Muhammad Wakil (Borno); Alhaji Abduljelili Oyewale Adesiyan (Osun); Ambasada Aminu Wali (Kano), da Hajiya Jamila Salik (kano).

Sai kuma Akon Etim Eyakenyi (Akwa Ibom); Lawrencia Labaran Malam (Kaduna); Dr T. W. Danagogo (Rivers); Asabe Asmau Ahmed (Niger) da Dr. Khaliru Alhassan (Sokoto).

Karin bayani