Shugaban Nijar na ziyara a Singapore

Image caption Shugaban Nijar, Mahamadou Issoufou.

Shugaban Jamhuriyar Nijar Alhaji Mahamadou Issoufou na wata ziyarar aiki a kasar Singapore.

Ana sa ran zai gana da shugaban kasar da Pirai ministansa a wani yunkuri na kulla hulda tsakanin kasashen biyu.

Dr Abarshi Magalma, masanin tattalin arziki a Nijar ya ce kulla hulda da kasashe masu tasowa na da matukar alfanu ga Nijar.

A cewarsa hakan zai ba Nijar mafita idan manyan kasashen duniya sun shiga matsala.

Haka kuma zai bata dabarun bunkasa arzikinta kasancewar irin wadannan kasashe basu dade da magance irin matsalolin da Nijar ke fama da su ba.

Karin bayani