An kashe masu rigakafin Polio a Pakistan

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Pakistan na cikin tsirarun kasashen da Polio ke yaduwa

'Yan bindiga a Pakistan sun harbe mutane uku har lahira a lokacin da suke yi wa yara rigakafin cutar Polio, wato shan Inna.

Rahotanni sun ce 'yan bindigar sun kashe mata biyu ne da namiji daya yayin da suke aikin rigakafin gida-gida a kokarin gwamnati na baya bayan nan na kawar da Polio daga kasar.

A baya dai 'yan Taliban sun yi ikirarin kashe masu rigakafin Polio saboda zargin da suke musu na yi wa kasashen ketare leken asiri.

Sun kuma ce su na zargin ana amfani da rigakafin ne don kashe sinadirin haihuwar 'ya'ya maza.

Pakistan na daya daga cikin tsirarun kasashen duniya da Polio ke cigaba da yaduwa.

Karin bayani